Nigerian news All categories All tags
Takarar su Atiku tana sama tana dabo a Jam’iyyar PDP

Takarar su Atiku tana sama tana dabo a Jam’iyyar PDP

- Wasu Matasa sun nemi su Atiku su hakura da takarar Shugaban kasa

- Matasan Arewar sun ce Gwamna Dankwambo ya dace da mulkin kasar

- Kungiyar tana ganin Alhaii Dankwambo Matashi ne kuma ya san aiki

Labari ya kai gare mu cewa wasu Matasan Arewa sun nemi irin su tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar da masu harin kujerar Shugaban kasa a 2019 su janye shirin su na takara su ba Gwamna Ibrahim Dankwambo dama.

Takarar su Atiku tana sama tana dabo a Jam’iyyar PDP

An kira Atiku su hakura da batun takarar Shugaban kasa a 2019

Wata Kungiya ta hadakar Matasan Yankin Arewa ta nemi Atiku Abubakar da kuma tsohon Shugaban PDP Sanata Ahmad Makarfi, da tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido su hakura da batun takara, su bi Gwamna Ibrahim Dankwambo.

KU KARANTA: Shugaba Buhari bai jin tsoron kowa a wajen takara – APC

Takarar su Atiku tana sama tana dabo a Jam’iyyar PDP

Matasa sun nemi Makarfi su janye shirin takara

Kungiyar ta nemi wadannan manyan ‘Yan PDP su marawa Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Ibrahim Dankwambo baya a zaben mai zuwa. Shugaban Kungiyar Matasan watau Kwamared Abdullahi Mohammed Jika ya fadi wannan.

Matasan sun ce babu wanda Najeriya ke nema yanzu irin Gwamnan na Gombe saboda kuruciyar sa da irin aikin da yayi a Jihar. Kungiyar Matasan tace Dankwambo mutum ne mi kishi kuma bai da nuna bambanci a lamarin Shugabancin sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel