Nigerian news All categories All tags
Obasanjo bai isa ya hana Buhari takara ba – Inji Jam’iyyar APC

Obasanjo bai isa ya hana Buhari takara ba – Inji Jam’iyyar APC

- Sakataren APC ya bayyana irin kokarin Shugaba Gwamnatin Buhari

- Mala Buni yayi magana game da wasikar Obasanjo ta kwanakin baya

- APC tace babu wanda ya isa ya hana Shugaba Buhari tsayawa takara

Jam’iyyar APC mai mulki tayi magana game da wasikar da tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya aikawa Shugaba Buhari inda tace duk da haka Obasanjo bai isa ya hana Buhari takara ba.

Obasanjo bai isa ya hana Buhari takara ba – Inji Jam’iyyar APC

Sakataren APC Buni yace Buhari bai jin tsoron kowa a 2019

Jam’iyyar mai mulki ta APC tayi wannan bayani ne ta bakin Sakataren ta Alhaji Mai Mala Buni wanda yayi hira da Jaridar Daily Trust. Sakataren na APC yace Obasanjo yana da daman bayyana ra’ayin sa kamar yadda Shugaba Buhari ke da damar kara takara.

KU KARANTA: Shugaban kasa Buhari ya samu karfin gwiwar takara a 2019

APC ta bayyana cewa Shugaba Buhari yayi fama da kalubalen tsaro da tattalin arziki kuma an samu nasara a wadannan bangarori. Mai Mala Buni yana ganin da gaskiya a bakin tsohon Shugaban kasa Jonathan da yace shekaru 4 sun yi kadan ayi gyara.

Sakataren Jam’iyyar dai yana ganin ba za a hada APC da tayi shekaru 3 a mulki da PDP da ta mulki kasar nan na sama da shekaru 15 ba. APC ta kuma bugi kirji tace ba ta shakkar fitowa takara da kowane idan har dai Shugaban kasa Buhari ke rike da tutar ta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel