Nigerian news All categories All tags
2019: ‘Yan Miyetti Allah sun tsaida ‘Dan takarar su na Shugaban kasa

2019: ‘Yan Miyetti Allah sun tsaida ‘Dan takarar su na Shugaban kasa

- Makiyayan kasar nan sun yi Gwamnatin APC mubaya’a

- Sama da Makiyaya 5000 sun nemi Buhari ya zarce a 2019

- Haka kuma Miyetti Allah tayi na’am da Gwamnan Bauchi

Mun ji cewa yayin da ake fara shiryawa zabe shekara mai zuwa na 2019, Makiyayan Kasar nan a karkashin Kungiyar ‘Yan Miyetti Allah sun tsaida ‘Dan takarar su na kujerar Shugaban kasa.

2019: ‘Yan Miyetti Allah sun tsaida ‘Dan takarar su na Shugaban kasa

Miyetti Allah sun yi na’am da tazarcen Buhari da Gwamna Abubakar

Makiyayan kasar nan da ke reshen Miyetti Allah su na bayan Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019. Haka kuma Kungiyar za ta marawa Gwamnan Bauchi Mohammed Abubakar baya a zaben da za ayi shekarar badi na 2019.

KU KARANTA: Ko Buhari zai sake tsayawa takara da Osinbajo a 2019

Sama da Makiyaya 5000 su ka jadadda goyon bayan su ga takarar Shugaba Buhari da kuma Gwamnan Jihar Bauchi Abubakar a zaben 2019 kwanan nan. Shugaban Kungiyar, Saleh Garba ya bayyaana wannan ga manema labarai.

Kungiyar Makiyayan sun yabawa kokarin wannan Gwamnatin ta APC musamman wajen habaka tattalin arzikin kasa da inganta tsaro. Makiyayan sun yabawa yunkurin hako man fetur a Jihar Bauchi da kuma sauran aikin Gwamnatin nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel