Nigerian news All categories All tags
Ba na kawo maganar 2019 a rai na yanzu – Inji Osinbajo

Ba na kawo maganar 2019 a rai na yanzu – Inji Osinbajo

- Mataimakin Shugaban kasa yace ba ya kawo batun zaben 2019

- Farfesa Osinbajo yace burin su cika alkawarin da su ka dauka

- Gwamnatin Shugaba Buhari tayi alkawarin gyara kasar a 2015

Mun ji cewa Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyanawa manema labarai cewa shi fa har yanzu ba ya kawo maganar zaben da za ayi a shekara mai zuwa na 2019 a ran sa.

Ba na kawo maganar 2019 a rai na yanzu – Inji Osinbajo

Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo tare da Buhari

Farfesa Yemi Osinbajo yace a yanzu haka ko kadan ba ya kawowa ran sa batun zabe. Mataimakin Shugaba Buharin yace abin da ke gaban sa shi ne cika alkawarin da su ka daukarwa ‘Yan Najeriya, kuma aka zabe shi da Buhari su yi a 2015.

KU KARANTA: Ba maganar tazarce ke gaban Shugaba Buhari ba – Osinbajo

Mataimakin Shugaban Najeriyar ya bayyana wannan ne lokacin da yake zantawa da ‘Yan jarida a Birnin Davos na Kasar Switzerland inda aka yi wani taro kan tatallin arziki. Osinbajo yace ba maganar sake takara da Buhari ne a gaban sa ba.

Osinbajo ya bayyana cewa Gwamnatin Buhari ta habaka tattalin arzikin kasar kuma tayi gyara a Najeriya duk da karancin kudin shiga kwarai da gaske. Yanzu haka Najeriya na cikin kasashen da su ka sharara da noman shinkafa a Duniya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel