Karin bayani: Harin Taliban a Kabul na dazu da safe, ya kashe mutum 95

Karin bayani: Harin Taliban a Kabul na dazu da safe, ya kashe mutum 95

- Kabul babban birnin Afghanistan na shan hare-hare daga kungyoyin 'yan ta'adda shekaru da dama

- An kai hain ne a yau da safe a mota da aka makalawa bam, kuma ya kashe mutane kusan 100

- Kungiyoyi masu zazzafan kishin Islama suna son kai hari wuraren da mutane kan shakata da sunan

Karin bayani: Harin Taliban a Kabul na dazu da safe, ya kashe mutum 95
Karin bayani: Harin Taliban a Kabul na dazu da safe, ya kashe mutum 95

Bayanai da ke fitowa bayan hare-haren da aka kai a Kabul babban birnin Afghanistan , a yau da safe, ya kashe akalla mutane 95, ya kuma raunata da dama kamar yadda majiyar mu ta ruwaito

A rahoton mu na dazu babu labarin wadanda suka rasu, sai dai masu rauni, sai a yanzu bayanai ke kara bayyana kan munin harin.

Kungiyar kishin addini ta Taliban ta ce ita ta kai harin wanda ya jikkata akalla mutane 158, bayan wadanda suka rasu din.

DUBA WANNAN: Taliban sun kai hari a babban birnin Afghanistan

Wadanda suka kai harin sun tuka wata motar daukar marasa lafiya ce da suka makare ta da bama-bamai, inda suka wuce wani wurin duba mutane da 'yan sanda suka kafa ba tare da an gane su ba.

Harin ya auku ne kusa da tsohon ginin ma'aikatar harkokin cikin gida, wanda ke kusa da ofisoshin Tarayyar Turai da Babbar Majalisar Zaman Lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng