Nigerian news All categories All tags
An saki Hamshakin Yariman Saudiyya, Waleed

An saki Hamshakin Yariman Saudiyya, Waleed

- An saki Waleed Bin Talal bayan ya yi kimanin watanni 3 a tsare

- Ya na daga cikin mutane 350 da a ka tsare su a wani Otel tun 4 ga watan Nuwamba

- An sake shi ne bisa yarjeniyar biyan fansa na makudan kudi

A ranar Asabar ne Masarautar Saudiyya ta saki Hamshakin Yariman Masarautar, Waleed Bin Talal, bayan ya yi kimanin watanni 3 a tsare. An sake shi ne bayan wani yarjeniyar fansa da ya biya.

An dai tsare Attajirin Yariman ne tare da wasu mutanen bisa zargin rashawa da wasu laifufukan masu alaka da hakan.

An sako Yariman kasar Saudiyya da aka tsare

An sako Yariman kasar Saudiyya da aka tsare

Waleed wanda a ke wa lakabi da ''Warren Buffet'' na Saudiyya, shi ne mafi sanuwa cikin mutane 350 da a ka tsare tun 4 ga watan Nuwamba na 2017, a Otel din Luxury Litz-Carlton da ke Riyadh.

KU KARANTA: Gwamnatin Kasar Sin ta kafa dokar hana karatun Kur'ani

Cikin wanda a ka tsare har da hamshakan ma su kudi da ministoci. Su din ma an sake su ne bisa yarjeniyar biyan makudan kudi a matsayin diyya. Waleed bai yi tsokaci ga manema labarai ba domin ba'a amince yayi hakan ba.

Wata majiya ta shaida cewar Alkalin Alkalan Masarautar, shi ne ya bayar da umurnin sakin na sa. Wata majiyar kuma ta ce an sake shi ne bisa yarjeniyar biyan miliyan 100 na dalar Amurka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel