Nigerian news All categories All tags
'Yansanda a Kaduna sun kwato turawan Afirka ta kudu da masu garkuwa suka sace

'Yansanda a Kaduna sun kwato turawan Afirka ta kudu da masu garkuwa suka sace

- An sace su a hanyar su ta zuwa wurin hakar ma'adinai a Kaduna

- Abba Kyari ne ya jagoranci aikin

- An chafke wadanda suka yi garkuwar da su

'Yansanda a Kaduna sun kwato turawan Airka ta kudu da masu garkuwa suka sace

'Yansanda a Kaduna sun kwato turawan Airka ta kudu da masu garkuwa suka sace

Wasu masu garkuwa da mutane da suka saci wasu mutanen Afirka ta kudu su 2, sun shiga hannu bayan da hukumar 'yansanda daga Abuja suka ceto wadanda suka kama din a yau dinnan.

An sace Thomas Arnold da Hendrick Gideon a 23 ga watan nan na Yanairu a wani kauye na Birnin Gwari da ake kira Maidoro, an ceto su tare da kame wadanda suka yi garkuwar da su kuma suka nemi kudaden fansa.

DUBA WANNAN: Atiku na fuskantar kalubale daga APC

Matsalar irin wannan kame da fansa dai ta zama ruwan dare musamman a jihar Kaduna, amma kuma da alama yanzu duk masu wannan sana'a sukan kare a shiga hannu bayan sun amshi kudin na fansa ko in sun yo waya.

Abba Kyari dai wani kwararren danSanda ne da ya kware wajen bin diddigi da kamo irin wadannan masu muguwar sana'a.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel