Nigerian news All categories All tags
Muhimman dalilai da ya sanya Buhari ya halarci taron AU a ƙasar Habasha

Muhimman dalilai da ya sanya Buhari ya halarci taron AU a ƙasar Habasha

A yau ne shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya fara gudanar da aikinsa na kwanaki hudu a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, domin halartar taron ƙungiyar shugabannin nahiyyar Afirka ta AU, inda zai kasance cikin kwamitin zaman lafiya da tsaro na mambobi 14 a matsayin wani jigo na ƙungiyar AU.

Babban hadimin shugaban ƙasa na musamman akan hulda da manema labarai, Mallam Garba Shehu ya bayyana cewa, taron zai tattauna dangane da tashin-tashina da kuma rikice-rikice a wasu sassan nahiyyar Afirka, sauye-sauyen yanayi da sakamakonsa da kuma ƙaruwar adadin 'yan gudun hijira tare da batun ababen dake kawo naƙasun ci gaban ƙasashen.

Shugaba Buhari a yayin tafiya kasar Habasha

Shugaba Buhari a yayin tafiya kasar Habasha

Mallam Garba yake cewa, wannan taro zai kuma yi nazari kan al'amurran ƙasashen Somalia, Sudan ta Kudu, Guinea Bissau, Jamhuriyyar Afirka ta Tsakiya da kuma Jamhuriyyar Dimokuradiyar Congo.

KARANTA KUMA: Koriya ta Arewa ta fara shirin yaƙin duniya na uku

Ya ƙara da cewa, taron zai kuma tattauna dangane da batutuwan yankin tafkin Chadi, ƙoƙarin kawo ƙarshen ta'addancin Boko Haram tare da al'amurran ƙasar Mali da yankin Sahel da suke ci gaba da ta'azzara duk da ƙokarin maƙotan ƙasashe da kuma majalisar dinkin duniya.

Legit.ng ta fahimci cewa, manufar wannan kwamiti shine gudanar da gargadi na farko da kuma ta hanyar diflomasiyya wajen kiyaye zaman lafiya tare da bayar da shawarwari ga ƙasashen AU domin inganta tsaro da hadin kai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel