Nigerian news All categories All tags
Ganduje ya kona muggan kwayoyi na naira biliyan 1 a Kano

Ganduje ya kona muggan kwayoyi na naira biliyan 1 a Kano

- Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya kona muggan kwayoyi da a ka kama har na naira biliyan 1

- Gwamnatin Jihar ta kuma habaka wuraren kula da tubabbun 'yan kwaya a Jihar

- Kwamandan NDLEA shi kuma jaddada kudirin Hukumar na tseratar Jihar daga muggan kwayoyi

A ranar Juma'a ne Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya kona muggan kwayoyi har na naira biliyan 1 wanda Hukumar Yaki da Safaran Kwayoyi (NDLEA), ta ka kama a wurare daban daban a Jihar.

Ganduje ya kona muggan kwayoyi na naira biliyan 1 a Kano

Abdullahi Umar Ganduje

An kona kwayoyin ne a harabar ofishin Hukumar. Ganduje ya bayyana cewar Jihar ta habaka wuraren kula da tubabbun 'yan kwaya. Ya kuma yi kira ga al'umma da su bayar da hadin kai wurin magance safaran kwayoyi.

DUBA WANNAN: Rikicin Makiyaya: Gwamnonin jihohin Binuwai, Ribas da Taraba sunyi wa Ministan Tsaro raddi

Ganduje ya kuma yi kira da a gaggauta hukunta ma su safaran kwayoyi da ke hannun hukuma, kuma a tsananta hukuncin na su.

Shi kuwa mai gudanar da wata Kungiyar Muryar Canji, Dakta clem Ohameze, ya yabawa NDLEA a kokarin da ta ke yi na yaki da safaran muggan kwayoyi. Haka zalika, ya yabawa gwamnati game da irin na ta kokarin.

Shi kuma Kwamandan NDLEA, Malam Hamza Umar, ya jaddada kudirin Hukumar na tabbatar da Jihar ta tsira daga muggan kwayoyi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel