Nigerian news All categories All tags
Ba na ra'ayin kujerar shugaban ƙasa - Gwamna Badaru

Ba na ra'ayin kujerar shugaban ƙasa - Gwamna Badaru

Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Abubakar Badaru ya bayyana cewa, ko kaɗan ba ya da sha'awar neman takarar kujerar shugaban ƙasa a zaɓen 2019.

Badaru ya kuma barrantar da kansa daga ƙungiyar dake angiza shi tare da goyon bayan sa wajen neman takarar kujerar shugabancin ƙasar nan a zaɓe mai gabatowa.

Gwamnan jihar Jigawa; Muhammad Abubakar Badaru

Gwamnan jihar Jigawa; Muhammad Abubakar Badaru

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata sanarwar ranar Asabar ta yau a birnin Dutse, da sanadin hadiminsa mai hulɗa da manema labarai, Mallam Bello Zaki.

KARANTA KUMA: Wata dattijuwa 'yar shekara 90 ta fara makarantar firamare

Mallam Bello yake cewa, "ko kaɗan gwamna Badaru ba ya da dangantaka da ƙungiyar dake angiza sa wajen hanƙoron kujerar shugaban ƙasa a sanadiyar bayyanar rubutacciyar wasiƙar tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo."

"A sakamakon haka ne gwamnatin jihar take kiran ɗaukacin al'ummar jihar da su yi watsi da wannan ƙanzon kurege da wasu ke ƙirƙira domin cimma manufa ta zalunci."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel