Nigerian news All categories All tags
Rikicin Makiyaya: Gwamnonin jihohin Binuwai, Ribas da Taraba sunyi wa Ministan Tsaro raddi

Rikicin Makiyaya: Gwamnonin jihohin Binuwai, Ribas da Taraba sunyi wa Ministan Tsaro raddi

- Gwamnonin Jihohin Binuwai, Ribas, Taraba da wasu kungiyoyi masu rajin kare hakin bil-adama a ranar Juma'a sunyi Allah wadai da kalaman Ministan Tsaro

- Sun zarge shi da rashin nuna damuwa da halin da mutanen da hare-haren ya shafi iyalinsu

- Gwamna Ortom ya cacaki Ministan Tsaron, inda ya ce yana daya daga cikin wadanda ke bawa Shugaba Buhari shawarwari marasa kyau

Gwamnonin Jihohin Binuwai, Ribas, Taraba da wasu kungiyoyi masu rajin kare hakin bil-adama a ranar Juma'a sunyi Allah wadai da kalaman Ministan Tsaro, Mansur Dan Ali game da musaababin rikicin Makiyaya da Manoma da ke faruwa a wasu sassan Najeriya.

A sanarwan da suka bayar ta bakunnan hadiman su na fanin kafafen yada labarai, Gwamnonin sun ce bayyanan da suka fito daga bakin Dan-Ali ya nuna cewa bai damu da halin da iyalan wanda sukayi rashin yan uwan su ke ciki ba.

Rikicin Makiyaya: Gwamnonin jihohin Binuwai, Ribas da Taraba sunyi wa Ministan Tsaro raddi

Ministan Tsaro

A hirar da Dan Ali ya yi da manema labarai, ya ce rufe hanyoyin da makiyaya ke bi don kiwon da kuma kafa dokar hana kiwo da wasu Jihohi sukayi ne ya jawo barkewar rikicin.

Gwamna Ortom ya cacaki Ministan Tsaron, inda ya ce yana daya daga cikin wadanda ke bawa Shugaba Buhari shawarwari marasa kyau. Ortom ya ce jihar sa ba ta da filayen da za ta bawa makiyaya.

DUBA WANNAN: Abun kunya ne yadda babu wata matatan man fetur da ke cikakken aiki a Najeriya, inji Shugaba Buhari

A gefe guda, Gwamna Darius Ishaku na jihar Taraba, wanda ya yi magana ta bakin hadimin sa na fanin yada labari Mista Bala Dan-Abu ya nuna takaicin sa yadda Dan-Ali ya ce dokar hana kiwo ne ya janyo rikicin, Gwamnan ya ce an rikicin na faruwa tun kafin kafa dokar hana kiwon, daga baya ne aka kafa dokan domin samar da tsaro da zaman lafiya.

Shima Gwaman Nyesome Wike na jihar Ribas ya nuna rashin jin dadin sa ga kalaman Ministan, ya ce idan ma dokar ba tayi wa wasu daidai ba, kamata yayi a zauna a tatauna domin samun mafita amma ba a fara kashe-kashe ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel