Nigerian news All categories All tags
Zaben 2019: Dole ne a yi wa 'yan takarar shugabancin kasa gwajin lafiya

Zaben 2019: Dole ne a yi wa 'yan takarar shugabancin kasa gwajin lafiya

A wani yunkuri na tabbatar da lafiyar shugabannin kasar Najeriya, kungiyar likitocin Najeriya da kuma likitocin kasashe rainon kasar Ingila sun bukaci a rika yi wa 'yan takara gwaji domin tabbatar da koshin lafiyar su.

A cewar kungiyoyin, wannan matakin idan har aka dauke shi to ba shakka zai taimake su wajen tabbatar da samun shugabannin kasa masu cikakkar lafiya da za su kai kasar ga tudun-ka-tsira.

Zaben 2019: Dole ne a yi wa 'yan takarar shugabancin kasa gwajin lafiya

Zaben 2019: Dole ne a yi wa 'yan takarar shugabancin kasa gwajin lafiya

KU KARANTA: Ka shirya mika mulki a 2019 - Ekweramadu zuwa ga Buhari

Legit.ng ta samu cewa kungiyoyin sun yi karin haske game da cewa duk da yake dai kowa zai iya yin rashin lafiya a kowane lokaci, amma sanin matsayin shugaban kasa kafin ya zama shugaban yana da matukar anfani.

A wani labarin kuma, Shugabannin sassan kasar nan na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a takaice sun bayyana rashin gamsuwar su bisa ga yadda shugaban jam'iyyar ke rike da jam'iyyar da suka ce hakan zai iya gurgunta su musamman ma yanzu da suke tunkarar zabe.

Shugabannin sannan dai shida na kasar sun bayyana hakan ne a cikin wata wasikar koke da suka aika wa shugabannin kwamitin aiwatarwa na jam'iyyar inda suka nuna matukar rashin dacewar shugaban da ya cigaba da jan ragamar su.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel