Nigerian news All categories All tags
An fara: Hukumar zabe ta INEC ta yi kashedi ga Atiku Abubakar kan 2019

An fara: Hukumar zabe ta INEC ta yi kashedi ga Atiku Abubakar kan 2019

- Bisa doka sai an bada izini jam'iyyu zasu fara kamfe, kuma ya zuwa yanzu ba'a bayar ba

- Saura shekara daya a yi zabuka na 2019 a kowanne mataki

- An ga fastocin Atiku Abubakar na yawo a birane

An fara: Hukumar zabe ta INEC ta yi kashedi ga Atiku Abubakar kan 2019

An fara: Hukumar zabe ta INEC ta yi kashedi ga Atiku Abubakar kan 2019

Alhaji Atiku Abubakar, tsohoon VP ga Obasanjo, ya koma jam'iyyar PDP inda ya ke neman takarar shugabanci kasar nan a karo na 6 tun bayan shigarsa siyasa.

Sai dai hakan ba bisa ka'ida bane inji hukummar INEC, domin a wannan lokaci, akwai jaddawali na lokuta da za'a ce masu takara su fara rawar siyasa. Kuma INEC din ce kadai zata bada wannan dama.

A ta bakin kwamishinanta na jiharsa ta Adamawa dai, Kassim Gaidam yayi kashedi kan yadda fastocin Alhaji Atikun da ma na gwamnan jihar Bindow, suka cika jihar ta Adamawa musamman babban birnin.

DUBA WANNAN: An yi kira ga shugaba Buhari da ya kawo karshen almajirci kaffin yace zayyi takara

A cewarsa dai, wannan ba bisa ka'ida bane, kuma dole ne su bari sai lokaci yayi su fara kamfe. Ya kuma yi kira ga jama'a da su zo su karbi katunan kuri'unsu, innda ya ce, akwai akalla katunan guda 94,000 da ba'a karba ba a jihar.

A kuma nasu bangaren, kungiyar Masihiyya ta CAN, ta koka kan yadda watakil masu gudun hijira daga gidajensu da ta'addanci ya kora da zasu kasa iya kada kuri'unsu muddin ba'a yi musu tanadi na musamman ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel