Nigerian news All categories All tags
Hadakar kungiyoyin sa-kai sunyi kira ga shugaba Buhari da ya kawo karshen almajircin yara kanana

Hadakar kungiyoyin sa-kai sunyi kira ga shugaba Buhari da ya kawo karshen almajircin yara kanana

- Kungiyar ta ce 'Almajirci zalunci ne da iyaye kan iyi wa 'ya'yayensu da sunan neman ilimin addini'

- Ana aiko yara birane su nema wa kansu abinci da rayuwa tun suna kanana

- Wasu sukan zama 'yan tasha ko masu ta'adda idan sun girma

Hadakar kungiyoyin sa-kai sunyi kira ga shugaba Buhari da ya kawo karshen almajircin yara kanana

Hadakar kungiyoyin sa-kai sunyi kira ga shugaba Buhari da ya kawo karshen almajircin yara kanana

Hadakar kungiyoyi da yawa na NGOs a fadin kasar nan, sun yi babban kira ga shugaba Muhammadu Buhari, da ya bar baya mai kyau kafin zaben 2019, ya samar da dokar da zata haramnta wa iyaye aiko 'ya'yansu bara tun suna kanana.

Kungiyoyin sun hada da Kungiyar masu sakulanci ta kasa, ta mulhidai da atishai, da na sadaka, a ciki da wajen Najeriya. Brighter Brains Institute a Amurka, Nigeria Humanists, Atheist Society, Lagos Humanists, Khalifa Dankadai Foundation, masu taimakon almajirai, da ma Hallmark Minds.

DUBA WANNAN: Yadda ake sace muku kudi baku sani ba

A sanarwar, wadda magatakardarta ya sanya wa hannu, Muhammadu Mubarak, ya ce an mayar da almajirai ne tamkar bayi ba 'yantattu ba, inda ake sakinsu daga gida, ba wani abinci, tufafi ko wuraren kwana.

Akalla yara miliyan gomma ne ke almajirci a arewar Najeriya, inji ma'aikatar ilimi ta tarayya, wadanda miliyan uku a Kano suke, inj gwamnan jihar a bara.

An dai dade ana kira ga hukumomi, na siyasa, masu mulki da ma na gargajiya da su yi hobbasa kan wannan tauye yara da ake yi a al'umma, amma kowannensu yayi biris.

Daga cikin wadanda zasu iya wani abu, akwai Shugaban kasa, Sarkin musulmi, Sarakunan arewa, Dattijai na yankin, majalisun jihohi da na tarayya, da kotuna da ma 'yansanda/hisba

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel