Nigerian news All categories All tags
Buhari ya shirya wa shan kashi a zaɓen 2019 - Ekweremadu

Buhari ya shirya wa shan kashi a zaɓen 2019 - Ekweremadu

A ranar Juma'ar da ta gabata ne, mataimakin shugaban majalisar dattijai, Ike Ekweremadu, ya kirayi shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, akan ya tabbatar gwamnatinsa ta gudanar da zaɓe na gaskiya da kuma adalci a shekarar 2019.

Ekweremadu ya kuma gargaɗi shugaba Buhari, akan ya kasance cikin shirin karɓar sakamakon zaɓen a kowane hali na nasara ko kuma kishiyar hakan idan shi da jam'iyyar sa suka sha kashi.

Mataimakin shugaban majalisar ya bayar da wannan shawara ne a sakamakon rashin jin daɗin sa da ya nuna dangane da yadda nahiyyar Afirka ke fuskantar barazana da kuma mummunan hatsari a tsarin tafiyarta ta dimokuraɗiyya.

Ike Ekweremadu

Ike Ekweremadu

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, mataimakin shugaban majalisar ya bayyana hakan ne a yayin gabatar da wata lacca akan siyasar Afirka a wurin wani taro da ya halarta a ƙasar Birtaniya.

KARANTA KUMA: Wani mahaifi ya kashe jaririnsa ɗan kwanaki biyar da haihuwa a jihar Bauchi

Ekweremadu ya gargaɗi dukkanin 'yan siyasar Afirka wajen haƙuri da kuma juriya akan sakamakon zaɓe a yayin da suka sha kashi, wanda da sanadin hadiminsa akan hulɗa da manema labarai, Uche Anichukwu, ya yaba wa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, da ya sanya Najeriya bisa turba ta dimokuraɗiyya a idon duniya, bayan ya sha kashi a zaɓen 2015 kuma ya karɓi sakamakon hannu biyu ba tare da wani tashin hankali ba.

Legit.ng ta fahimci cewa, a sanadiyar haka ne mataimakin shugaban majalisar dattawa ta Najeriya, yake kira ga shugaba Buhari da kuma dukkanin 'yan siyasa a Afirka, akan su yi haƙurin jurewa rashin nasarar zabe, domin hakan shi zai ƙara musu mutunci da kuma kima a idon duniya baki ɗaya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel