Nigerian news All categories All tags
Malabu: Kachiku ya roki Buhari ya bar wa Shell da ENI rijiyar mai

Malabu: Kachiku ya roki Buhari ya bar wa Shell da ENI rijiyar mai

- An taka cuwa-cuwa kan rijiyar mai ta Malabu OML 245

- An gaji da shari'a an koma sulhu na bayan fage

- Ana hakar mai ganga dubban daruruwa a rana daga rijiyar ta Malabu

Malabu: Kachiku ya roki Buhari ya bar wa Shell da ENI rijiyar mai

Malabu: Kachiku ya roki Buhari ya bar wa Shell da ENI rijiyar mai

Karamin ministan man fetur Mista Kachikwu, ya shawarci shugaba Buhari da ya barwa kamfanin mai na Shell da na ENI makekeyiyar rijiyar mai ta Malabu domin sulhu, bisa yarjejeniya da aka cima ta bayan fage, a wajen kotu.

Wannan na zuwa ne bayan da takardun ofishin antoni janar da suka tsiyayo aka ji a jaridu, ke nuna babu wata kwakkwarar hujja da ke nuna za'a iya kama tsofin manyan ma'aikata da suka yi badakalar ta dala bilyan daya ta dalar Amurka, kusan Naira biliyan 400 kenan.

DUBA WANNAN: Yadda ake sace muku kudi ko aler baku ji

Shi dai Malami, yace ko anje kotu ba lallai ayi nasara ba, banda ma uban kudi da aka kashe da lokaci da aka bata shekaru.

Ita dai rijiyar ta Malabu, OML 245, na samar da makudan kudaden danyen man fetur kuma an sayar wa da kamfunnan ne a rahusa, a yadda ake zargi, domin wasu su sami kuudin ta hanyar cin hanci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel