Nigerian news All categories All tags
'Yan Jam'iyyar PDP sun roki Makarfi ya fito takaran Shugabancin Kasa a 2019

'Yan Jam'iyyar PDP sun roki Makarfi ya fito takaran Shugabancin Kasa a 2019

- Jam'iyyar PDP reshen Jihar Kaduna ta shawarci Ahmad Makarfi ya fito takaran Shugabancin Kasar nan

- Tsohon Gwamnan Jihar, Ramalan Yero, ya ce Makarfi ne ya fi cancanta da iya tafiyar da Kasar nan

- Yero ya ce ba don Makarfi ba, da jam'iyyar PDP ta zama tarihi

A ranar Juma'a ne reshen PDP na Jihar Kaduna ta shawarci Ahmad Makarfi da ya fito takaran Shugabancin Kasa a 2019. Ta yi masa alkawarin ba shi goyon baya idan har ya fito. 'Yan Jam'iyyar ne su ka bayyana hakan a wani taro da su ka gudanar.

'Yan PDP sun roki Makarfi ya fito takaran Shugabancin Kasa a 2019

'Yan PDP sun roki Makarfi ya fito takaran Shugabancin Kasa a 2019

'Yan Jam'iyyar sun ce Makarfi shi ne ya fi cancanta da iya tafiyar da wannan Kasa ta mu. Tsohon Gwamnan Jihar, Ramalan Yero, yayin jawabi a taron, ya yabawa Makarfi game da yadda ya tafiyar da jam'iyyar a matsayin shugaban ma su kula da ita.

DUBA WANNAN: Ministan Tsaro ya bayyana musabbabin kashe-kashen da ke faruwa

Yero ya ce Makarfi ya yi abun a zo a gani wurin shawo kan matsalolin jam'iyyar da kuma gudanar da taron jam'iyyar na Kasa. A cewar Yero, ba don Makarfi ba, da jam'iyyar PDP ta zama tarihi.

Kamfanin Dillancin Labarai (NAN), ta ruwaito cewar yero ya nemi 'yan jam'iyyar su marawa Makarfi baya, wanda hakan kuwa akasarin su ka yi. NAN ta yi hasashen cewa idan har Makarfi ya amince ya fito, to lallai zai yi karon batta da irin su Atiku Abubakar da Sule Lamido da Ibrahim Shekarau.

Shugaban jam'iyyar na Jihar, Hassan Hyat, ya ce an yi taron ne don tattauna yadda za a fuskanci zaben 2019. Hyat ya yaba da yawan 'yan jam'iyyar da su halarci taron, musamman mata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel