Nigerian news All categories All tags
Yan sanda bakwai, soji biyu sun rasa rayukansu sandiyar rikicin manoma da makiaya a jihar Adamawa

Yan sanda bakwai, soji biyu sun rasa rayukansu sandiyar rikicin manoma da makiaya a jihar Adamawa

Birgediya kwamandan 23rd Amour Brigade Yola, Bello Mohammad, yace jami’an yan sanda bakwai da soji biyu sun rasa rayukansu cikin watanni biyu sanadiyar rikicin makiyaya da manoma a garin Numan.

Birgediya Janar Mohammad, ya ce hukumar tsaro ta shirya taro domin jan kunne na karshe ga wadanda ke wannan aika-aika saboda idan kunne ya ji, gangan jiki ya tsira.

“Rikicin da ya faru a Numan da makwabta ya yadu zuwa karamar hukumar hudu Girei, Demsa and Lamurde,da kuma wasu sassan jihar Taraba.

“Abin takaici, matakan da jami’an tsaro suka dauka bai haifi da mai ido ba har yanzu; masu wannan abu sun dauki sassucinmu a matsayin gazawa wajen gudanar da aikinmu.

Yan sanda bakwai, soji biyu sun rasa rayukansu sandiyar rikicin manoma da makiaya a jihar Adamawa

Yan sanda bakwai, soji biyu sun rasa rayukansu sandiyar rikicin manoma da makiaya a jihar Adamawa

“Amma daga yanzu, mu mambobin hukumar tsaro sunhada karfi da karfe wajen dakile wannan tashin-tashina da kashe-kashe.

“Mataki na farko na muka dauka domin kawar da wannan abu shine gudanar da taron gangamin. Yana daga cikin matakan ruwan sanyin ake dauka wajen tabbatar da tsaro, sannan muyi amfani da karfin soja.”

KU KARANTA KUMA: Sanata Lado ya sauya sheƙa a yayin da Kwankwaso zai ziyarci jihar Kano

A karshe Janar Mohammed ya soki masu kudi, yan siyasa, sarakunan gargajiya akan rashin daukan wani mataki akan wannan abu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel