Nigerian news All categories All tags
Bakin ciki ya kashe wata mata bayan da Yansanda suka yi ram da ɗanta ba cas, ba as

Bakin ciki ya kashe wata mata bayan da Yansanda suka yi ram da ɗanta ba cas, ba as

Wata mata mai shekaru 42m Asiata Adeyanju ta yanke jiki ta fadi tsabar bakin ciki, biyo bayan cafke danta mai shekaru 17 da jami’an hukumar Yansanda masu yaki da yan fashi da makami, SARS.

The Nation ta ruwaito yansandan sun kama matashi mai suna Muiz ne a gidansa dake kan titin Ajenifuja, a unguwar Ilupeju na jihar Legas, a yayin da yake kokarin tayar da na’aurar samar da wutar lantarki, Janareta.

KU KARANTA: A kori Buhari: Obasanjo zai kaddamar da tafiyar hadakar jiga jigan yan siyasa da zasu kawar da Buhari a sati mai zuwa

Bakin ciki ya kashe wata mata bayan da Yansanda suka yi ram da ɗanta ba cas, ba as

Daga hagu: Muiz, Mahaifiyarsa da Mijinta

Majiyar Legit.ng ta ruwaito tafiya da Yaron ke da wuya, sai mahaifiyarsa ta fito a guje tana kuwwa tana binsu a guje, a garin haka ne ciwon hawan jininta ya tashi, nan fa ta yanke jiki ta fadi ta garzaya barzahu.

Rahotanni sun bayyana cewa mijin matar, Musendiku Adeyanju ne ya kwaci yaron daga hannun jami’an Yansandan bayan ya kaste sallarsa, kuma ya roke su cewar a yanzu haka an garzaya da matarsa Asibiti don duba halin da ta shiga biyo bayan yanke jiki da ta yi sakamakon kama shi.

Shi ma Mu’iz ya tabbatar ma majiyar mu cewa yana kokarin tayar da janareta ne sai kawai ya ji an cakume shi ta baya, suka ce masa ya shiga motarsu, sa’annan a hanya ma sun kakkama mutane da dayawa. Tuni aka yi ma Matar jana’iza kamar yadda Musulunci ya tanadar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel