Nigerian news All categories All tags
Ministan Tsaro ya bayyana musabbabin kashe-kashen da ke faruwa

Ministan Tsaro ya bayyana musabbabin kashe-kashen da ke faruwa

- Ministan ya ce Dokar Hana Yawon Kiwo da toshe hanyoyin da makiyaya ke bi shi ne musabbabin kashe-kashen

- Ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala taron harkar tsaro da a ka yi a Fadar Shugaban Kasa

A ranar Alhamis ne Ministan Tsaro, Mansur Dan Ali, ya bayyana cewar dokar hana yawon kiwo da kuma toshe hanyoyin da makiyaya ke bi, su ne musabbabin kashe-kashen da ke faruwa a 'yan kwanakin nan, musamman a Jihohin Benue da Taraba.

Ya bayyana hakan ne ga manema labarai jim kadan bayan kammala taron Hukumar Tsaro na Kasa da a ka yi Fadar Shugaban Kasa, wanda Shugaban Kasan ya jagoranta.

Kafa dokokin hana kiwo ne ya janyo rikicin makiyaya, inji Ministan tsaro

Kafa dokokin hana kiwo ne ya janyo rikicin makiyaya, inji Ministan tsaro

KU KARANTA: Kotu ta yi watsi da karar da Nnamdi Kanu ya shigar kan Hukumar Soji

Dan Ali ya kuma bayyana cewar ba zai yiwu a takura 'yan kasa ko a tauye ma su hakkokin su na kasancewa 'yan Kasa ba sannan a yi tsammanin za su koma gefe su yi shiru. Don haka dole ne mu yi hakurin zama da junan mu.

Sai dai kuma ya ce ba ya na goyon bayan kashe-kashen ba ne, ya na dai bayyana sababi ne. Ya kuma ce jawabin sa bai sha karo da jawabin gwamnati ba na cewar tsagera 'yan haure ne ke yin kashe-kashen, don kuwa su din ne ke yi, in ji shi.

Ya ce lamarin kashe-kashen ne a ka tattauna a taron da kuma maganar sayarwa Najeriya da jiragen ''Super Tucano A29'' guda 12 da Amurka za ta yi, da wadansu makaman na daban.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel