Nigerian news All categories All tags
Kotu ta yi watsi da karar da Nnamdi Kanu ya shigar kan Hukumar Soji

Kotu ta yi watsi da karar da Nnamdi Kanu ya shigar kan Hukumar Soji

- Bayan an dauki watanni ba'a ji mostsin sa, Nnamdi Kanu ya sake shigar da kara Kotu

- Yana nemi Kotun ta daura wa Shugaban Hafsoshin Sojin Kasa alhakin kawo shi Kotu a maimakon wadanda suka lamunce masa wurin karbar belli

- Kotun ta yi watsi da karar, inda ta ce babu wata hujja da ke nuna cewa Hukumar Sojin ne suka tsare shi

Babban Kotun Tarayya da ke Abuja tayi watsi da karar da shugaban kungiyar masu fafutukan kafa kasar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, inda ya ke bukatar Kotu ta daura wa Shugaban Hafsoshin Sojan Najeriya nauyin kawo shi Kotu.

A yayin da ta ke yanke hukunci kan karar da ya shigar ranar Juma'a, Mai Shari'ah Binta Nyako ta ce Kanu bai nuna wa Kotu wata hujja da ke bayyana cewa Hukumar Sojin Najeriya ne ta ke rike dashi, hasali ma babu wata hujja da ke nuna cewa an gan shi tare da wani Soja.

Kotu ta yi watsi da karar da Nnamdi Kanu ya shigar kan Hukumar Soji

Kotu ta yi watsi da karar da Nnamdi Kanu ya shigar kan Hukumar Soji

A cewar ta, hakan ya sa dole Kotu tayi fatali da karar da ya shigar. Nyako da kuma yi nuni da cewa Mista Kanu da kan sa ne ya shigar da karar, saboda haka ta yi mamakin yadda mutumin da yake ikirarin an sace shi kuma zai iya rubuto kara da kansa.

DUBA WANNAN: Gwamnan APC na jihar Filato, ya ki wa shugaba Buhari biyaya kan ware filin makiyaya

Lauya mai kare wanda ake tuhuma, Mista Ifeanyi Ejiofor ya tambayi kotu abin da zai yi domin wanda ya ke kare wa ya hallarci kotu a ranar da za'a saurari karar amma Kotu ta ce masa abinda ta sani shine an bawa wanda ake tuhuma belli kuma idan bai bayyana a Kotu ba rannar sauraron karar sa, wadanda suka tsaya ma sa ne za su kawo shi.

Mista Kanu da yana ikirarin cewa Hukumar Sojin Najeriya ne ta sace shi a ranar 14 ga watan Satumbar 2017 ranar da ta kai samame gidan sa.

Za'a cigaba da sauran karar na Nnamdi Kanu ne a ranar 20 ga watan Febrairun 2018.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel