Nigerian news All categories All tags
Zaben 2019: Eweremadu ya ba shugaba Buhari babban aiki kan zabe mai adalci da gaskiya

Zaben 2019: Eweremadu ya ba shugaba Buhari babban aiki kan zabe mai adalci da gaskiya

- A kullun ana ci gaba da samun cece-kuce game da zaben 2019 a Najeriya

- Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ike Ekweremadu ya bi sahun tafka muhawaran

- Ekweremadu ya fi maida hankali akan zabe mai inganci

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari day a tabbatar da cewa gwamnatinsa ta gudanar da zabe mai gaskiya da inganci a 2019.

Ya kuma shawarci shugaban kasar da shirya karban sakamakon zaben idan har shi ko jam’iyyar APC ta gaza yin nasara a zaben shugabancin kasa mai zuwa.

Zaben 2019: Eweremadu ya ba shugaba Buhari babban aiki kan zabe mai adalci da gaskiya

Zaben 2019: Eweremadu ya ba shugaba Buhari babban aiki kan zabe mai adalci da gaskiya

Ya fadi hakan ne duk da kokawa da yayi akan wannan cuta dake damun yankin Afrika, wanda ya bayyana a matsayin babban kalubale ga damokradiyyan Afrika.

KU KARANTA KUMA: Obasanjo na neman jam’iyyar da zai dunga juyawa ne - Keyamo

Ya ba da wannan shawarar ne yayinda yake Magana a malisar Amurka, inda ya bayar da wani darasi mai taken “Siyasar Afrika: Sauye-sauye da darusa” wato “African Politics: The Dynamics and Lessons.”

Ya jadadda cewa ya zama dole Najeriya ta zamo abun koyi ga sauran kasashen Afrika, sannan kuma ta zamo abun darajawa a idanun duniya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel