Nigerian news All categories All tags
Obasanjo na neman jam’iyyar da zai dunga juyawa ne - Keyamo

Obasanjo na neman jam’iyyar da zai dunga juyawa ne - Keyamo

- Festus Keyamo ya zargi Olusegun Obasanjo da kokarin ganin ya na juya wata jam’iyyar siyasa

- Ya ce tsohon shugaban kasar bai zamu damar mulkar PDP da APC ba

Babban lauyan Najeriya, Festus Keyamo ya caccaki tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo akan wasikar da aika ga shugaban kasa Muhammadu Buhari inda ya bukace shi da kada ya sake takara a 2019.

Obasanjo ya bayyana cewa jam’iyyar All Progressives Congress ta gaza a kasar yayinda ya kuma zargi jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da cin hanci da rasahawa da kuma rashin kwarewa.

Obasanjo na neman jam’iyyar da zai dunga juyawa ne - Keyamo

Obasanjo na neman jam’iyyar da zai dunga juyawa ne - Keyamo

Ya ba da shawarar kafa sabuwar kungiya a Najeriya wacce yake ganin ita zata magance matsalolin da kasar ke fuskanta.

KU KARANTA KUMA: 'Yan Najeriya mazauna Saudiyya sun yi Allah wadai da kalaman Sheik Ahmad Gumi

Keyamo ya je shafinsa na twitter inda ya zargi tsohon shugaban kasar da neman wata jam’iyya da zai juya.

Ya ce Obasanjo ya gane cewa ba zai iya juya jam’iyyar APC da PDP ba don haka yake kokarin kafa sabuwar jam’iyya da zai mulka son ransa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel