Nigerian news All categories All tags
A kori Buhari: Obasanjo zai kaddamar da tafiyar hadakar jiga jigan yan siyasa da zasu kawar da Buhari a sati mai zuwa

A kori Buhari: Obasanjo zai kaddamar da tafiyar hadakar jiga jigan yan siyasa da zasu kawar da Buhari a sati mai zuwa

Wata sabuwar tafiya data kunshi jiga jigan siyasan Najeriya za ta fito a ranar 31 ga watan Janairu a karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo, inji rahoton Premium Times.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Obasanjo ya nada tsohon gwamnan jihar Osun, Olagunsoye Oyinlola a matsayin shugaban tafiyar, sa’annan don gudun samun Baraka a gaba, za’a nada masu magana da yawun tafiyar a kowanne matsayi.

KU KARANTA: Rikicin makiyaya da manoma :Yan bindiga sun halaka Yansanda 7, Sojoji 2 a jihar Adamawa

Manufar tafiyar shi ne ta samar da wata sahihin hanya don kawar da gwamnatin shugaban kasa Muhammdu Buhari, kuma za’a kaddamar da kungiyar ce a babban birnin tarayya Abuja.

A kori Buhari: Obasanjo zai kaddamar da tafiyar hadakar jiga jigan yan siyasa da zasu kawar da Buhari a sati mai zuwa

Obasanjo

Idan za’a tunam Obasanjo ya bayyana gazawar gwamnatin Najeriya a karkashin shugaba Buhari, inda ya nuna sakacin ta wajen barin jami’an gwmanati suna tafka kura kurai ba tare da wani hukunci ba, haka zalika ya bayyana Buhari a matsayin mutum mai nuna son kai, don haka ya bukaci Buhari kada ya sake tsayawa takara.

Rahotanni sun nuna akwai akalla gwmanoni guda bakwai, Sanatoci ashirin da kuma yan majalisu guda 100 dake mara ma tsohon shugaba Obasanjo baya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel