Nigerian news All categories All tags
Rikicin makiyaya a jihar Binuwai: Gwamna Ortom ya caccaki ministan tsaro na Najeriya

Rikicin makiyaya a jihar Binuwai: Gwamna Ortom ya caccaki ministan tsaro na Najeriya

Gwamnan jihar Benuwe Samuel Ortom, ya soki ministan tsaro na Najeriya, Mansur Dan Ali, dangane da furucin sa na ɗora alhakin kashe-kashen makiyaya a jihar a sanadiyar ƙaddamar da dokar hana kiwo tun a shekarar 2017.

Ortom ya bayyana wannan batu a matsayin rashin tausayi, inda ya ƙara da cewa, furucin mai girma ministan tsaro shi yake nuna tabbacin babu wata mahanga anan kurkusa ta yin adalci akan waɗanda ibtila'in harin ya afkawa.

Rahotanni da sanadin Channnel TV sun bayyana cewa, Dan Ali ya yi wannan furuci ne a yayin taron zaman majalisa da shugaba ƙasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadarsa ta Abuja a ranar Alhamis ɗin da ta gabata.

Gwamna jihar Benuwe, Samuel Ortom

Gwamna jihar Benuwe, Samuel Ortom

Dan Ali yake cewa, kashe-kashen da suka afku a kwanan nan ya zamto wani ɓangare na tattaunawa a zaman majalisa da aka gudanar, inda yace shawarar kafa hukumar hana yaɗuwar makamai ta kasance ɗaya daga cikin matakan da gwamnatin tarayya ta ɗauka don magance tashin tashina a ƙasar nan.

KARANTA KUMA: Sanata Lado ya sauya sheƙa a yayin da Kwankwaso zai ziyarci jihar Kano

A yayin mayar da martani, gwamna Ortom ya bayyana cewa, matuƙar irinsu ministan tsaro zasu ci gaba da kasancewa a kujerar shugabanci wajen baiwa gwamnati gurguwar shawara, to ko shakka babu na ranar magance matsalolin tsaro da ƙasar nan take fuskanta.

Legit.ng ta fahimci cewa, gwamna Ortom ya bayyana hakan a ranar Juma'a ta yau, a yayin da yake tofa albarkacin bakinsa akan tuhumar hukumar DSS na cewar ƙungiyar ISIS ke da alhaki kashe kashen da suka afku a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel