Nigerian news All categories All tags
Ziyarar Kwankwaso: Kada ka kuskura ka shigo Kano ko ka hadu da fushin mu – Yansanda ga Kwankwaso

Ziyarar Kwankwaso: Kada ka kuskura ka shigo Kano ko ka hadu da fushin mu – Yansanda ga Kwankwaso

Rundunar Yansandan jihar Kano ta gargadi tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da ya dakatar da ziyarar da ya shirya kaiwa jihar Kano a ranar 30 ga watan Janairu.

Kwamishinan Yansandan jihar, Rabiu Yusuf ne ya bayyana haka ga manema labaru, idan yace matukar Kwankwaso ya dage akan shiga jihar, toh lallai doka za tayi aiki akansa, don kuwa zai gamu da fushinsa.

KU KARANTA: Jihohi guda 16 sun amince a tsugunar da Makiyaya da dabbobinsu a cikinsu, ga jerin su nan

Daily Trust ta ruwaito Kwamishinan yana fadin: “Babu shakka Kwankwaso a matsayinsa na dan kasa yana ikon shirya taro, da kuma ikon shiga duk inda ya ga dama, sai dai bayanai da muka samu sun nuna cewa jama’an jihar Kano na dar-dar da ziyarar da zai kawo, haka zalika akwai yiwuwar wasu yan siyasa ka iya amfani da damar wajen aikata aika aika.

Ziyarar Kwankwaso: Kada ka kuskura ka shigo Kano ko ka hadu da fushin mu – Yansanda ga Kwankwaso

Ganduje da Kwankwaso

“Don haka rundunar Yansandan jihar Kano na shawartar Kwankwaso da ya janye ziyarar nan tasa, har sai hankula sun kwanta, kuma an magance duk wasu barazanar tsaro dake tattare da ziyarar.” Inji shi

Daga karshe kwamishinann yace rundunar Yansanda c eke da hakkin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, don haka duk wanda ya nemi tada tsaye ko ya lalata zaman lafiya a jihar Kano zai gamu da fushin hukumar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel