Nigerian news All categories All tags
To fa: An haramtawa ‘yan majalisu sanya kayan da suke nuna alamar addini

To fa: An haramtawa ‘yan majalisu sanya kayan da suke nuna alamar addini

Majalisar dokokin Faransa ta haramtawa ‘yan majalisun kasar sanya kayan da suke nuna alamar addini, a karkashin wani sabon tsarin ko dokar fayyace irin kayan da zasu rika shiga zauren majalisar da su.

Majalisar dokokin Faransa ta kafa doka wadda ta haramtawa ‘yan majalisun dokokin kasar sanya kayan da suke nuna alamar addini, wannan dokar dai tana karkashin wani sabon tsarin fayyace irin kayan ko alama da zasu rika shiga zauren majalisar da su.

Legit.ng ta tattaro cewa, tuni dai matakin ya fara fuskantar suka daga bangarori daban daban a Faransa.

Shugaban majalisar dokokin Faransa, Francois de Rugy, ya kare wannan matakin inda ya bayyana cewa, bai take hakkin kowane dan majalisar ba, amma wani bangare ne daga cikin dokar da aka kafa ta shekarar 2004, da ta haramtawa malaman makarantu da daliban kasar sanya dukkanin wata kaya ko alama ta nuna addinin su.

To fa: An haramtawa ‘yan majalisu sanya kayan da suke nuna alamar addini

Zauren majalisar dokokin kasar Faransa

KU KARANTA: Abin da ya sa Obasanjo ya aikawa Shugaba Buhari wasika – Keyamo

A yanzu haka dai wasu ‘yan siyasar kasar na goyon bayan wannan matakin na majalisar Faransa da kuma neman a fadada shi zuwa jami’o’i da wuraren aiki a duk fadin kasar, wasu na kallon matakin ta fuskar cewa wani yunkuri ne kawai na fadada dakile ‘yancin addini.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel