Nigerian news All categories All tags
Kasar Sin ta horas da 'yan Najeriya sama da 3,600 sana'o'i daban-daban

Kasar Sin ta horas da 'yan Najeriya sama da 3,600 sana'o'i daban-daban

- Al'umman Najeriya da dama sun amfana da horo kan sana'o'i daban- daban daga kasar Sin

- Sun sami horon ne karkashin wata yarjejeniyar hadin gwiwa da akayi tsakanin kasashen guda biyu

- Sakamakon yarjejeniyar, Kasar ta Sin ta saka jari na N2.7bn a Najeriya tun shekarar 2006

'Yan Najeriya sama da 3,600 suka samu horo a kan sana'o'i daban-daban da Gwamnatin kasar Sin ta dauki nauyi cikin shekaru goma sha biyu da suka wuce.

Jami'in tattalin arziki na ofishin jakadancin kasar Sin a Najeriya, Mista Zhao Linxiang ne ya bayyana hakan a wata liyifa da aka shirya domin wadanda suka amfana da shirin a ranar Alhamis a garin Abuja.

Kasar Sin ta horas da 'yan Najeriya sama da 3,600 sana'o'i daban-daban

Kasar Sin ta horas da 'yan Najeriya sama da 3,600 sana'o'i daban-daban

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa (NAN) ta tattaro cewa al'umman sun sami horon ne kakashin wata yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu wanda aka fara a shekarar 2005 domin kara dankon zumunci tsakanin kasashen biyu.

DUBA WANNAN: Hukumar Sojin Kafa ta damke mutane 11 saboda bacewar wani soja

Mista Linxiang ya kara da cewa an shirya kwasa-kwasai kan aikin noma da kuma sadarwa a shekarar 2017 a garin Abuja. Ya kuma kara da cewa hadin kai tsakanin kasashen biyu ya haifar da alkhairi sosai.

Ya kuma bayyana cewa 'yan kasar Sin sun saka jari na misalin naira biliyan 2.7 a Najeriya tun kulla yarjejeniyar. Haka zalika, ya kuma ce Najeriya ce babbar abokiyar huldar kasuwancin kasar Sin ta 3 a duniya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel