Nigerian news All categories All tags
Rundunar yan sanda sun kama mai damfarar mutane a katin ATM a jihar Bauchi (hoto)

Rundunar yan sanda sun kama mai damfarar mutane a katin ATM a jihar Bauchi (hoto)

Rundunar yan sandan jihar Bauchi ta cafke wani matashi da ya shahara wajen damfarar mutane a layin ATM.

An cafke matashin mai suna Abdullahi Buhari mai shekaru 27 da ya fito daga yankin titin gidan Zoo a Kano ne a makon da ya gabata, bayan da dubun sa ta cika a wata na’urar cire kudi na bankin Union lokacin da yayi yunkurin wankar wani mai suna Dauda Habila dan shekara 37.

Matashin ya sanar da cewa sun jima suna damfarar mutane a bakin ATM da nufin zasu taimake musu wajen cire kudi, inda da zarar ka mika musu katin ATM dinka, sai su sauya maka shi da wani daban, wanda kuma iri daya ne da na bankin da kake amfani da shi.

Rundunar yan sanda sun kama mai damfarar mutane a katin ATM a jihar Bauchi (hoto)

Rundunar yan sanda sun kama mai damfarar mutane a katin ATM a jihar Bauchi

Bayan sun yi musayar katin, sai su rike lambobin sirri da kake amfani da su wajen cire kudi, sai su je wata na'urar cire kudin su tatse dan abin dake cikin asusun ajiyar naka.

KU KARANTA KUMA: Ku kama sannan ku hukunta duk wanda aka samu da makamai ba bisa ka’ida ba – Buhari ga hukumomin tsaro

An kama shine da katin ATM har guda ashirin kuma na bankuna daban-daban, da kuma katin dan kasa guda biyu mallakar wani mai suna Bashir Bala da kuma layin MTN guda biyu.

Daga karshe hukumar 'yan sandan jihar Bauchi, ta bakin kakakinta, Kamal Datti Abubakar ta yi kira ga masu cirar kudi a bakin ATM da su daina saurin yadda da mutanen da suka hadu da su a bakin na'urar cirar kudin musamman wadanda suka zo da sunan za su taimaka musu wajen cire kudi. Maimakon haka gara ka kira ma'aikatan bankin su taimaka maka.

Kakakin ya kuma kara da cewa nan ba da jimawa ba za su mika wanda ake zargin zuwa kotu domin yanke masa hukuncin da ya dace.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel