Nigerian news All categories All tags
Abin da ya sa Obasanjo ya aikawa Shugaba Buhari wasika – Keyamo

Abin da ya sa Obasanjo ya aikawa Shugaba Buhari wasika – Keyamo

- Festus Keyamo ya fadi abin da ya sa Obasanjo ya rubutawa Buhari wasika

- Babban Lauyan yace Obasanjo na neman wanda zai rika juyawa ne a mulki

- Keyamo yace har gobe tsohon Shugaban kasa Obasanjo ba zai bar siyasa ba

Ku na da labarin wasikar da tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya rubutawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari. Wani babban Lauya ya tona asirin Obasanjo game da wannan wasika.

Abin da ya sa Obasanjo ya aikawa Shugaba Buhari wasika – Keyamo

Obasanjo na neman Shugaban da zai rika juyawa ne - Keyamo

Festus Keyamo SAN wanda babban Lauyan kasar nan ne yayi karin haske game da wasikar inda yace yana da ra’ayin Obasanjo mutum ne mai neman wanda zai juya a kan mulki don haka ya rubutawa Shugaba Buhari wannan takarda.

KU KARANTA: Miyetti Allah sun fallasa dalilin da ya sa Obasanjo ya juyawa Buhari baya

Keyamo ya kara da cewa tsohon Shugaban kasar ba zai iya barin siyasa ba har gobe kuma ya san ba shi da wata ta-cewa a Jam’iyyar APC da PDP don haka ya fara kira a shirya wani gangami wanda dai duk a je a dawo shi zai dama.

Babban Lauyan yace tun da Oluesgun Obasanjo yayi yunkurin kara wa’adi na uku wanda aka taka masa burki yake neman yadda zai samu shugaban kasar da zai rika juyawa. Keyamo ya bayyana wannan ne a shafin sa na Tuwita dazu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel