Nigerian news All categories All tags
An kashe wasu Makiyaya da dabbobin su a Kamari Chaiwai

An kashe wasu Makiyaya da dabbobin su a Kamari Chaiwai

- Ana zargin an kashe wasu Makiyaya a Kamari Chaiwai

- Har ta kai dabbobin wadannan Bayin Allah ba a bari ba

- Idris Ahmad na CUPS ya kai wannan kuka a Facebook

Mun samu labari cewa ana zargin an yi wasu Fulani Makiyaya mugun barna a garin Kamari Chaiwai da ke cikin Jihar Filato inda aka hallaka wasu Makiyaya 2 aka kuma ga bayan dabbabin su.

Kungiyar CUPS ta bayyana wannan a shafin ta na Facebook. Kawo yanzu dai ba mu tabbatar da wannan rahoto ba. An kashe mutane 2 ne masu suna Anas Zakariya da kuma wani Musa Idris a tsakiyar makon nan da rana tsaka.

KU KARANTA: Makiyaya sun kashe wani Dan Sanda a Benuwe

Ana zargin wannan abu ya faru ne a Karamar Hukumar Bassa da kimanin karfe 3:00 na rana. Rahoton ya bayyana cewa har shanun wadannan mutane ba a bari ba. Ba dai yau ‘Yan Kabilar Irigwe su ka saba wannan barna ba.

Haka zalika kuma mun ji cewa an tsinci gawan wani Makiyayi a Yankin Kubwa da ke cikin babban Birnin Tarayya Abuja a karshen makon nan. Ba mamaki wasu ne su ka hallaka shi a cikin daji.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel