Nigerian news All categories All tags
PDP na Kogi ta yi wa Gwamnan Jihar tas bisa kudirin sa na samar da filayen kiwon shanu

PDP na Kogi ta yi wa Gwamnan Jihar tas bisa kudirin sa na samar da filayen kiwon shanu

- Jam'iyyar ta PDP ta amincewa da kudirin Gwamnatin Tarayya na samar da filayen kiwon shanu da Gwamnan ya yi ba dai dai ba ne

- Ta kuma ce ba za ta amince da mika filayen noma ga makiyaya ba, kuma ba za ta taba abincewa da wannan kudiri ba

- Mai magana da yawun jam'iyyar na Jihar, Mista Bode Ogunmola, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai

Jam'iyyar adawa, PDP, reshen Jihar Kogi, ta yi wa Gwamnan Jihar, Yahaya Bello, tas game da kudirin sa na kaddamar da shawaran da Gwamnatin Tarayya ta yanke na samar da wuraren kiwon shanaye a Jihar.

PDP na Kogi ta yi wa Gwamnan Jihar tas bisa kudirin sa na samar da filayen kiwon shanu

PDP na Kogi ta yi wa Gwamnan Jihar tas bisa kudirin sa na samar da filayen kiwon shanu

Mai magana da yawun jam'iyyar ta PDP, Mista Bode Ogunmola, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Alhamis a Lokoja, Babban Birnin Jihar. Ogunmola ya ce abin takaici ne yadda Gwamnan ya yanke wannan shawaran shi kadai, ba tare da tunbubar kowa ba.

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya ta umurci a sa ido a kan wasu sanannun 'yan Najeriya a kafafen sada zumunta

Ya kuma ce hakan bai dace ba a irin wannan lokaci da a ke zargin Fulani Makiyaya da aikata ta'addanci. Bugu da kari, hatta sauran Gwamnonin APC ba su amince da wannan kudiri ba.

Ogunmola ya ce wannan kudiri barazana ne ga harkar tsaro. Don haka su na bukatar Gwamnan ya canja shawara. A cewar sa, ba za su mika filiyen noman su ga makiyaya ba, kuma ba za su taba amincewa da wannan kudiri ba.

A cewar PDP, shekaru 2 da Gwamna Yahaya Bello ya yi cike su ke da abubuwan sa ba su yi wa al'umma dadi ba a rai. Haka zalika babu wasu ayyuka kwarara da za a iya nunawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel