Nigerian news All categories All tags
Ana zargin Makiyaya da kashe wani ‘Dan Sanda a Benuwe

Ana zargin Makiyaya da kashe wani ‘Dan Sanda a Benuwe

- Makiyaya sun kara hallaka wasu mutane a Jihar Benuwe

- Daga cikin wadanda aka kashe har da wani ‘Dan Sanda

- Gwamnan Jihar yace ba zai yi tsit ba sai ya ga an yi adalci

Mun samu labari cewa ana zargin Makiyaya da kashe wani Jami’in ‘Dan Sanda da wani Bawan Allah a Benuwe. Har yau dai an gaza shawo karshen rikicin Makiyaya cikin Kasar nan. Gwamnan yace dole ayi maganin wannan barna.

Ana zargin Makiyaya da kashe wani ‘Dan Sanda a Benuwe

An rasa lokacin da za a kawo karshen rikicin Makiyaya

Mutane 2 su ka bakunci lahira a hannun wasu da ake zargi Makiyaya ne a karamar Hukumar Guma da ke Jihar Benuwe. Wannan abu ya fari ne a daren Laraba ko kuma da safiyar ranar Alhamis. Gwamnan Jihar ya tabbatar da wannan.

KU KARANTA: An sace wani Sojan Najeriya a Jihar Adamawa

A jiyan ne Sanatan Jihar Kano Injiya Rabiu Kwankwaso ya ziyarci Jihar domin jajantawa Jama’ar Yankin. Gwamna Ortom yace kwanan nan an hallaka wasu manoma da kuma Bayin Allah da dama a babban birnin Jihar na Benuwe

Gwamnan ya zargi Makiyaya ‘Yan Kautal Hore da aikata wannan tabargaza kuma ya cigaba da kira a damke su. Gwamnan yace ba zai daina nemawa mutane sa hakkin su ba. An dai yi barnar ne lokacin da manoma su ka girbe amfanin gonar su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel