Nigerian news All categories All tags
Ku bar ni in fallasa Obasanjo kan wasikar da ya aikawa Buhari — Orji Kalu

Ku bar ni in fallasa Obasanjo kan wasikar da ya aikawa Buhari — Orji Kalu

Tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu ya caccaki tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo kan wasikar da ya aika ma shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Orji Kalu ya bayyana cewa shi zai tona asirin miyagun laifukan Olusegun Obasanjo.

A cewarsa yana da hujjoji kan yadda tsohon shugaban kasar ya karkatar da makudan kudade har dala biliyan 16 da sunan aikin samar da hasken wutar lantarki a lokacin da yake kan mulki.

Ya kara da cewa tsohon shugaban kasar ya aika laifukan rashawa da dama a lokacin mulkin nasa.

KU KARANTA KUMA: Ku kama sannan ku hukunta duk wanda aka samu da makamai ba bisa ka’ida ba – Buhari ga hukumomin tsaro

Kamar yadda Legit.ng ta kawo maku a baya, tsohon shugaba Obasanjo ya shawarci shugaba Buhari da kada ma yayi tunanin sake takarara a zaben 2019.

A cewar Obasanjo shugaba Buhari bai tabuka komai ba tunda ya hau mulki inda ya ambaci wasu laifan shugaban kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel