Nigerian news All categories All tags
An yi ram da mutane 11 bayan wani Sojan kasa ya bace

An yi ram da mutane 11 bayan wani Sojan kasa ya bace

- Rundunar Sojin Najeriya na neman wani Sojan ta a Adamawa

- Hakan ya sa aka kama wasu mutane har da wani Mai Unguwa

- Mutane dai na ta barin Opallo kar ace su fito da Sojan da ya bata

Mun samu labari daga Jaridar Premium Times cewa an yi ram da wasu mutane a Jihar Adamawa a dalilin wani babban Jami’in Soja da ya bace a wani kauye mai suna Opallo da ke cikin Karamar Hukumar Lamurde a Jihar.

Shugaban Rudunar Sojojin kasar da ke Jihar Adamawa watau Birgediya-Janar Bello Mohammed ya bayyana wannan. Daga cikin wadanda aka kama har da wani Mai Gari guda. Sai dai ba a bayyana sunan mai martabar ba.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya sa kafar wando guda da masu shigo da makami Najeriya

Janar Bello Mohammed yace yanzu an saki Mai Garin da sharadin zai nemo wadanda su ka sace Sojan kasar. Sarkin Bachama Honest Irimiya ya nemi a saki Mai Garin. Yanzu dai an bazama neman Sojan kasar a Yankin.

Jama’a da ke Kauyen na Opallo wanda ke karamar Hukumar Lamurde sai tserewa su ke yi inji manema labarai domin gudun Rundunar Sojojin Najeriya su bi ta kan su. Yanzu haka ‘Yan bidiga sun kona wani yanki na Garin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel