Nigerian news All categories All tags
Buhari ya ci mutuncin 'yan Najeriya a mayar da martani ga kalamun Obasanjo – In ji Junaid Muhammed

Buhari ya ci mutuncin 'yan Najeriya a mayar da martani ga kalamun Obasanjo – In ji Junaid Muhammed

Dan majalisar tarayyar Najeriya a Jamhuriyyar ta biyu, Dr. Junaid Muhammed, ya caccaki gwamnatin tarayya dangane da martani a kan maganganun Obasanjo, cewa ba zai yiwu a kalubalanci gaskiya ta hanyar karya ba.

Tsohon dan majalisar tarayyar Najeriya a Jamhuriyyar ta biyu, Dr. Junaid Muhammed, ya lura da cewa amsawar da gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta bayar dangane da sanarwar tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ba ta yi bayani a kan cin hanci da rashawa a cikin gwamnatin yanzu ba.

Majiyar Legit.ng ta tabbatar cewa, Muhammadu ya bayyana irin wannan martani a matsayin rashin kyautatawa da cin mutunci ga fahimtar 'yan Najeriya.

Yayin da yake amsa tambaya daga jaridar Punch, tsohon dan majalisar ya ce shugaba Buhari ya kasa magance manyan batutuwa musamman wanda suka shafi abotaka a gwamnatinsa, wanda tsohon shugaban ya bayyana.

Buhari ya ci mutuncin 'yan Najeriya a mayar da martani ga kalamun Obasanjo – In ji Junaid Muhammed

Tsohon dan majalisar tarayyar Najeriya a Jamhuriyyar ta biyu, Dr. Junaid Muhammed

Ya ce, "Wannan martanin cin mutunci ne ga 'yan Najeriya. Gwamnatin tarayya ba za ta iya zargin cewa mutum kamar Obasanjo sungularsa ya hana shi sani abin da gwamnatin ke yi”.

KU KARANTA: Ba maganar tazarce ke gaban Shugaba Buhari ba – Osinbajo

"Wannan ba zai iya kasance kariya ga rashin daidaito da cin hanci da rashawa a gwamnatin tarayya ba”.

"Zan iya baku jerin mukamai a cikin wannan gwamnati wanda ba bisa ga cancanta ba amma a kan wasu sharudda. Ba zaku iya kalubalanci gaskiya ta hanyar karya ba", in ji shi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel