Nigerian news All categories All tags
Yan bindiga sun kai hari ofishin 'yan sanda sun fitar da wadan da aka tsare

Yan bindiga sun kai hari ofishin 'yan sanda sun fitar da wadan da aka tsare

Wasu hatsabiban da ba san ko suwaye ba sun afkawa ofishin 'yan sanda na Ojodu Abiodun dake a karamar hukumar Ifo ta jihar Ogun a jiya Lahadi inda suna yi mummunar barna tare da fitar da dukkan wadada ke saye a bayan kanta.

Haka nan kuma mun samu cewa hatsabiban sun kwashi makamai da kuma bindigogi masu tarin yawan da ba'a kammala sanin adadin su ba sannan kuma suka kone motoci da dama.

Yan bindiga sun kai hari ofishin 'yan sanda sun fitar da wadan da aka tsare

Yan bindiga sun kai hari ofishin 'yan sanda sun fitar da wadan da aka tsare

KU KARANTA: Jam'iyyu 30 sun sha alwashin korar Buhari daga Villa a 2019

Legit.ng ta samu a wani labarin kuma cewa, Akalla mutane uku suka sha harsashen bindigar jami'an 'yan sandan nan na Najeriya ya runduna ta musamman dake yaki da fashi da makami watau Special Anti-Robbery Squad, SARS shiyyar jihar Plateau, garin Jos a wata mashayar jiya.

Lamarin dai kamar yadda muka samu daga majiyoyin sun tabbatar da cewa ya faru ne a ranar Litinin din da ta gabata kuma wadanda aka harba din sun hada da Dung Chung, dan shekaru 42 dake sana'ar kafinta.

Sauran kuma sun hada da Dung Chollom da ba'a tantance adadin shekarun sa ba sannan kuma karmin su da ake kira Junior. Yanzu haka dai mun samu cewa an sallami biyu daga cikin su yayin da dayan kuma har yanzu yana asibiti.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel