Nigerian news All categories All tags
Dattijan Yarbawa sun caccaki ministan sadarwa game da fara yi wa Buhari kamfe

Dattijan Yarbawa sun caccaki ministan sadarwa game da fara yi wa Buhari kamfe

Kungiyar nan ta dattijan jama'ar kabilar yarbawa a Najeriya ta bayyana takaicin ta ga halin da ministan sadarwa na shugaba Buhari kuma mamba a majalisar zartarwar Najeriya watau Adebayo Shittu game da riga malam masallacin da yayi na fara yi wa shugaba Buhari kamfe din zaben 2019.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa an ruwaito ministan ya halarci taron majalisar zartarwar na sati-sati da da ake gudanarwa a fadar shugaban kasar ta Najeriya da kayayyakin kamfe din shugaba Buhari inda kuma ya kuduri aniyar rarraba su.

Dattijan Yarbawa sun caccaki ministan sadarwa game da fara yi wa Buhari kamfe

Dattijan Yarbawa sun caccaki ministan sadarwa game da fara yi wa Buhari kamfe

KU KARANTA: EFCC ta daskarar da asusun ajiyar Babachir Lawal

Legit.ng ta samu cewa sai dai hakar ta sa bata cimma ruwa ba bayan da bai samu goyon bayan abokan aikin na sa ba game da yin hakan.

A wani labarin kuma, Tsohon kakakin majalisar tarayyar Najeriya a bangaren majalisar wakillan Mista Dimeji Bankole zai jagoranci wasu mutane akalla 32 wajen yunkurin kawar da shugaba Buhari daga kujerar sa a zaben 2019 mai zuwa.

Wannan yunkurin dai kamar yadda muka samu daga majiyoyin mu zai faru ne a jam'iyyar adawa ta Action Democratic Party, ADP a takaice da tsohon kakakin ke da matsayi na masu ruwa-da-tsaki.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel