Nigerian news All categories All tags
Farashin gangar mai ta kai $71 karon farko tun kafin hawan Buhari

Farashin gangar mai ta kai $71 karon farko tun kafin hawan Buhari

Labarin da muke samu daga majiyoyin mu na nuni da cewa kawo yanzu dai farashin gangar danyen mai ta tashi ya zuwa akalla $71 a karon farko tun kafin shugaba Buhari ya anshi karagar mulki a shekarar 2014.

A shekarar ne dai da 2014 farashin danyen man yayi faduwar tsohuwar guzuma wanda hakan ne kuma ya nemi durkusar da tattalin arzikin Najeriya tare kuma da yin matukar barazana ga darajar kudaden mu.

Farashin gangar mai ta kai $71 karon farko tun kafin hawan Buhari

Farashin gangar mai ta kai $71 karon farko tun kafin hawan Buhari

KU KARANTA: Jam'iyya 30 sun shirya korar Buhari a 2019

Legit.ng ta samu cewa da wannan ne dai 'yan Najeriya ke ta kara sa ran wata kila lamurra su dan kara canzawa tare da kara kyau musamman ma game da farashin kayan masarufi da kuma tattalin arzikin su.

A wani labarin kuma, Wata gamayyar jam'iyyun adawa a Najeriya da a kwanan baya cikin watan Yulin shekarar bara suna kaddamar da wata hadaka domin samowa kasar Najeriya tabbataccen cigaba ta sha alwashin tsayar da dan takarar da zai kayar da Buhari a zaben 2019.

Mai magana da yawun hadakar ne dai da ke zaman shugaban daya daga cikin jam'iyyun kuma watau jam'iyyar National Conscience Party, NCP mai suna Dakta Yunusa Tanko ya bayyana wa manema labarai wannan kudurin na su.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel