Nigerian news All categories All tags
Jami'an 'yan sandan Najeriya sun bindige wasu mutane 3 a mashaya, garin Jos

Jami'an 'yan sandan Najeriya sun bindige wasu mutane 3 a mashaya, garin Jos

Akalla mutane uku suka sha harsashen bindigar jami'an 'yan sandan nan na Najeriya ya runduna ta musamman dake yaki da fashi da makami watau Special Anti-Robbery Squad, SARS shiyyar jihar Plateau, garin Jos a wata mashayar jiya.

Lamarin dai kamar yadda muka samu daga majiyoyin sun tabbatar da cewa ya faru ne a ranar Litinin din da ta gabata kuma wadanda aka harba din sun hada da Dung Chung, dan shekaru 42 dake sana'ar kafinta.

Jami'an 'yan sandan Najeriya sun bindige wasu mutane 3 a mashaya, garin Jos

Jami'an 'yan sandan Najeriya sun bindige wasu mutane 3 a mashaya, garin Jos

KU KARANTA: 'Yan Najeriya miliyab 50 sun tsayar da Buhari takara a 2019

Sauran kuma sun hada da Dung Chollom da ba'a tantance adadin shekarun sa ba sannan kuma karmin su da ake kira Junior. Yanzu haka dai mun samu cewa an sallami biyu daga cikin su yayin da dayan kuma har yanzu yana asibiti.

A wani labarin kuma Hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake yaki da cin hanci da rashawa tare da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau Economic and Financial Crimes Commission, EFCC ta daskare asusun ajiyar kudi na banki mallakin tsohon Sakataren gwamnatin tarayyar, Mista Babachir Lawal.

Wannan dai kamar yadda muka samu daga majiyar mu mataki ne da hukumar ta dauka musamman ma domin samun sukunin cigaba da binciken da suke yi masa na handame kudin kasa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel