Nigerian news All categories All tags
2019: Dalilin da yasa bai kamata Igbo su amince da maganganun Obasanjo ba – In ji Okwara

2019: Dalilin da yasa bai kamata Igbo su amince da maganganun Obasanjo ba – In ji Okwara

Wani shugaban ‘yan kabilar Igbo ya bukaci al’ummar su yi watsi da maganganun tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo su marawa shugaba Buhari baya a zaben 2019, inda ya ce bayan Buhari yankin ne zai samar da shugaban kasa na gaba.

Wani dattijon ‘yan kabilar Igbo a jihar Imo, Mista Livinus Okwara, ya bayyana a ranar Alhamis, 25 ga watan Janairu cewa, ya kamata al'ummar Igbo su marawa shugaba Muhammadu Buhari baya a babban zabe na shekara ta 2019, inda ya kara da cewa bayan Buhari yankin kudu maso gabashin kasar ne zai samar da shugaban kasa na gaba.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari , dattijon ya mayar da martani ga wata sanarwa da tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo ya yi, inda ya shawarci shugaba Buhari kada ya nema tsayawa takara karo na biyu a zaben shekara ta 2019.

Okwara ya ce: "Ya kamata mutanenmu su yi hankali da wannan mutumin. Ban ma san irin qiyayyar da yake yi a kanmu ba. Ina so in gaya muku cewa Obasanjo bai damu ba game da ci gaban Najeriya, duk abin da yake kokarin yi shi ne ya ci gaba da kasacewa a harkokin gwamnatin Najeriya".

2019: Dalilin da yasa bai kamata Igbo su amince da maganganun Obasanjo ba – In ji wani shugaban Igbo

Shugaba Muhammadu Buhari da shugabannin 'yan kabilar Igbo

"Jam'iyya mai mulki ta APC, ita ce hanyar da ta fi dacewa kuma ta hanyar da ‘yan kabilar Igbo za su iya kai ga samun shugabancin Najeriya, don haka duk wani shiri bayan wannan zai iya kasance kalubale ga wani mutumin Igbo ya kai ga shugabancin kasar a shekara ta 2023”, in ji shi.

KU KARANTA: 'Yan Najeriya miliyan 50 sun tsayar da Buhari takarar tazarce a 2019

Ya ce shugaba Buhari ne kadai mutumin da yake da kyakyawar nufi ga al’ummar kasar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel