Nigerian news All categories All tags
2019: Jam'iyyu 30 sun sha alwashin tsayar da dan takara daya da zai kayar da Buhari

2019: Jam'iyyu 30 sun sha alwashin tsayar da dan takara daya da zai kayar da Buhari

Wata gamayyar jam'iyyun adawa a Najeriya da a kwanan baya cikin watan Yulin shekarar bara suna kaddamar da wata hadaka domin samowa kasar Najeriya tabbataccen cigaba ta sha alwashin tsayar da dan takarar da zai kayar da Buhari a zaben 2019.

Mai magana da yawun hadakar ne dai da ke zaman shugaban daya daga cikin jam'iyyun kuma watau jam'iyyar National Conscience Party, NCP mai suna Dakta Yunusa Tanko ya bayyana wa manema labarai wannan kudurin na su.

2019: Jam'iyyu 30 sun sha alwashin tsayar da dan takara daya da zai kayar da Buhari

2019: Jam'iyyu 30 sun sha alwashin tsayar da dan takara daya da zai kayar da Buhari

KU KARANTA: Rundunar soji ta damke mutane 11 bisa batan abokin aikin su

Legit.ng ta samu haka zalika cewa shugaban na National Conscience Party ya kuma tabbatar da cewa a sati mai zuwa, ranar Talata zasu ida sanar da yan Najeriya dukkan matsayar da suka cimmawa a zaben na 2019 mai zuwa.

A wani labarin kuma, Labarin da muke samu daga majiyoyin mu na nuni da cewa kawo yanzu dai farashin gangar danyen mai ta tashi ya zuwa akalla $71 a karon farko tun kafin shugaba Buhari ya anshi karagar mulki a shekarar 2014.

A shekarar ne dai da 2014 farashin danyen man yayi faduwar tsohuwar guzuma wanda hakan ne kuma ya nemi durkusar da tattalin arzikin Najeriya tare kuma da yin matukar barazana ga darajar kudaden mu.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel