Nigerian news All categories All tags
'Yan Najeriya miliyan 50 sun tsayar da Buhari takarar tazarce a 2019

'Yan Najeriya miliyan 50 sun tsayar da Buhari takarar tazarce a 2019

Akalla 'yan Najeriya kimanin mutane miliyan 50 ne masu sana'ar saye-da- sayarwar tireda ne a karkashin inuwar kungiyar National Harmonised Traders Union, a turance suna sanar da ba shugaban kasar Najeriya dukkanin cikakken goyon baya a zaben 2019 mai zuwa.

Shugaban kungiyar ne dai kamar yadda muka samu bayani daga majiyar mu mai suna Dakta Bature Abdulaziz ya sanar da hakan a yayin wani taron manema labarai da ya shirya a garin Kano dake arewa maso yammacin Najeriya.

'Yan Najeriya miliyan 50 sun tsayar da Buhari takarar tazarce a 2019

'Yan Najeriya miliyan 50 sun tsayar da Buhari takarar tazarce a 2019

KU KARANTA: Dalar AMurka ta fadi a kasuwar 'yan canji a Najeriya

Legit.ng ta samu cewa Dakta Bature haka zalika ya bayyana cewa sun cimma wannan matsayar ne tare da dukkan daukacin mambobin kungiyar na kasa baki daya dake a dukkan jahohin kasar nan biyo bayan nazarin tsanaki da suka yi wa salon mulkin na shugaba Buhari din.

A wani labarin kuma, Da alama dai dangantaka ta so tayi tsami bayan da kasar Najeriya ta sanar da kin amincewar ta game da wasu sharudda da kasar Amurka ta gindaya mata bisa kudurin ta na sayen jiragen yaki daga kasar ta kamar dai yadda ministan tsaro, Mansur Dan-Ali ya sanar.

Mun samu dai cewa minista Mansur Dan-Ali dai ya bayyana cewa majalisar zartaswar kasar nan a baya ta amince da kudi zunzurutu da suka kai $494 miliyan domin sayen jiragen yakin a baya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel