Nigerian news All categories All tags
Abin da ya sa na gana da Maina a Kasar waje – Ministan shari'a Malami

Abin da ya sa na gana da Maina a Kasar waje – Ministan shari'a Malami

- Shugaban kasa Buhari ya san da maganar Maina inji Malami

- Ministan shari’a yace bai yi da-na-sanin ganawa da Maina ba

- Batun Maina ya kawo surutu sosai ga Gwamnatin na Buhari

Mun ji cewa Ministan shari’a na kasa Abubakar Malami SAN ya bayyana abin da ya sa ya hadu da Mista Abdurrasheed Maina kwanaki a Birnin Dubai duk da akwai wasu tarin zargi a kan sa na lamushe dukiyar Gwamnati a kokacin Jinathan.

Abin da ya sa na gana da Maina a Kasar waje – Ministan shari'a Malami

Buhari ya san abin da ya faru tsakani Maina da Malami

Ministan kasar yace bai yi da-na-sanin abin da yayi ba ko kadan don kuwa a cewar sa ba zai ki neman ganawa da irin su Maina ba idan har zai samu karin bayani game da abubuwan da za su taimakawa Najeriya da ‘Yan kasa.

KU KARANTA: Mai ba Gwamnan Legas Ambode shawara, Tinubu ya rasu

Ana zargin Maina da satar wasu Biliyoyin kudi da aka ware na ‘yan fansho sai kuma ga shi ya dawo Najeriya bayan da ya tsere har ya koma ofis bayan sun gana da Ministan Buhari. Wannan dai ya jawo korafi kwarai da gaske.

Ministan a wata hira da yayi da wata Mujalla ya bayyana cewa Shugaban kasa Buhari ya san da batun Maina bayan haduwar ta su. Malami yace yayi hakan ne don ganin an yi maganin satar wasu kudin fansho da ake yi a Gwamnati.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel