Nigerian news All categories All tags
Babban mashawarcin gwamnan Legas ya yanke jiki ya mutu a gasar sada zumunta

Babban mashawarcin gwamnan Legas ya yanke jiki ya mutu a gasar sada zumunta

- Babban mashawarci ga gwamnan jihar Legas ya yanke jiki ya mutu a wani gasar sada zumunta

- Mashawarcin ya mutu ne a ranar Alhamis yayin wani gasar sada zumunta a yankin Epe na jihar

- Manyan jami’an gwamnatin jihar sun kasance a wannan gasar da aka hada a Epe

Babban mashawarci ga gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode a kan cinikayya, Deji Tinubu, ya mutu.

An tattara cewa Deji, wanda shi ne tsohon shugaban hukumar kula da wasanni na jihar Legas, ya mutu a yammacin ranar Alhamis, 25 ga watan Janairu yayin wani gasar sada zumunta a yankin Epe da ke jihar.

‘Yan majalisar zartarwa na jihar Legas da wasu manyan jami’an gwamnati sun halarci wannan taron shakatawa a Epe.

Babban mashawarcin gwamnan Legas ya yanke jiki ya mutu a gasar sada zumunta

Babban mashawarci ga gwamnan jihar Legas a kan ciniki, Deji Tinubu

KU KARANTA: Rubdugu! Duba wadanda suka alkawarin marawa Obasanjo baya don korar APC daga Aso Rock

Legit.ng ta tattaro cewa Tinubu ya fadi ne a filin wasan, sa’a nan aka tabbatar da mutuwarsa a wani asibiti a Epe.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel