Nigerian news All categories All tags
Gwamnatin Tarayya ta umurci a sa ido a kan wasu sanannun 'yan Najeriya a kafafen sada zumunta

Gwamnatin Tarayya ta umurci a sa ido a kan wasu sanannun 'yan Najeriya a kafafen sada zumunta

- Ta umurci Hukumomin Tsaro da su ido musamman a kafafen sada zumunta don magance matsalar yada kalaman kiyayya

- Ta yi wannan umurni ne yayin wani taron harkar tsaro da a ka gudanar a Fadar Shugaban Kasa

- Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, shi ne ya jagoranci zaman tattaunawar

Gwamnatin Tarayya ta umurci Hukumomin Tsaro da su sa ido a kan wadan su sanannun 'yan Najeriya musamman a kafafen sada zumunta na yanar gizo don magance yada kalaman kiyayya.

An bayar da wannan umurni ne a wani taro na harkar tsaro da a ka yi a Fadar Shugaban Kasa, wanda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Gwamnatin Tarayya ta umurci a sa ido a kan wasu sanannun 'yan Najeriya a kafafen sada zumunta

Gwamnatin Tarayya ta umurci a sa ido a kan wasu sanannun 'yan Najeriya a kafafen sada zumunta

Wannan umurni ya zo shekara 1 kenan bayan Ministan Labarai, Lai Mohammed, ya yi alkawarin cewa wannan Gwamnatin ba za ta taba sa ka takunkumi ba a kafafen sada zumunta na yanar gizo.

DUBA WANNAN: Hukumar soji ta damke mutane 11 da a ke zargin da hannun su cikin bacewar soja

Ministan Tsaro, Mansur Dan Ali, ya bayyana cewar yada kalaman kiyayya da batanci a filayen sada zumunta abu ne mai ban takaici. Don haka Hukumomin Tsaro su sa ido don magance matsalar.

Bugu da kari, an kuma tattauna a kan Jirage da a ke kira ''Super Tucano A29'', a kan dalar Amurka miliyan 495. Za a biya kudin jiragen ne ya zuwa 20 ga watan Fabrairu na 2018. Sai dai kuma sai 2020 sannan Jiragen za su shigo hannu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel