Nigerian news All categories All tags
Hukumar Sojin Kafa ta damke mutane 11 saboda bacewar wani soja

Hukumar Sojin Kafa ta damke mutane 11 saboda bacewar wani soja

- Hukumar ta damke mutane 11 da a ke zargin da hannun su cikin bacewar sojan a kauyen Apollo a Jihar Adamawa

- Cikin su harda wani Hakimi na Masarautar Bachama ta Karamar Hukumar Lamurde ta Jihar

- Wata runduna ta Hukumar Sokin ta bazama don neman sojan da ya bata

Kwamandan wata Rundunar Sojin Kafa, Birgediya Janar Bello Mohammed, ya bayyana cewar sun damke mutane 11 da a ke zargin akwai hannun su cikin batar wani soja a kauyen Apollo da ke Karamar Hukumar Lamurde na Jihar Adamawa.

Hukumar Sojin Kafa ta damke mutane 11 saboda bacewar wani soja

Shugaban Hukumar Sojin kasa, Buratai

Mohammed ya bayyanawa manema labarai a ranar Alhamis cewar cikin wadanda a ka kama har da wani Hakimi, amma dai kuma ba a bayyan sunan Hakimin ba.

DUBA WANNAN: Makiyaya da su ke kai mana hari baki ne ba 'yan gari ba, in ji Sarakunan Gargajiya na Filato

Sai dai kuma an sakinHakimin bisa roko da Sarkin Bachama ya yi, Honest Irimiya, ya na mai daukan alkawarin zai tsamo wadanda su ka aikata laifin.

Kwamandan ya kuma bayyana cewar tuni wata rundana na Sojin ta bazu don neman sojan da ya bace a yanki. Su kuwa mazauna yankin sai tserewa su ke saboda tsoron ka da a kama su.

Wadansu mazauna garin kuwa sun yi ikirarin cewar 'yan bindiga sun kone wani sashi na yankin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel