Nigerian news All categories All tags
An fara: Katsina ta ware hekta-5,300 saboda makiyaya da shanunsu

An fara: Katsina ta ware hekta-5,300 saboda makiyaya da shanunsu

- Gwamnatin Jihar Katsina ta ba kyautar fili mai girman kadada 5300 domin kiwo

- Ana neman kowacce jiha ta ware filayen domin a girke shanu su dena yawo

- Rikicin makiyaya na kawo matsalar kashe-kashe a kasa

An fara: Katsina ta ware hekta-5,300 saboda makiyaya da shanunsu

An fara: Katsina ta ware hekta-5,300 saboda makiyaya da shanunsu

Gwamnatin jihar katsina ta ba da fili mai girman kadada 5,300 a kauyen Gurbin Baure dake karamar hukumar Jibia, domin kiwo ga fulani.

A wata ganawa da manema labarai Babban mai bawa gwamna shawara a bangaren noma, Dokta Abba Yakubu Abdallah, yace gwamna masari ne ya jagoranci shirin bada filin.

DUBA WANNAN:

A cewar sa, gwamnati ta bada kyautar filin tun baya da shekara daya da ta wuce, saboda kokarinta na inganta noma da kiwo. 

Idan ba a mance ba gwamnatin tarayya ta bada umarnin bawa fulani filin kiwo, a kokarin da take na neman mafita akan rikicin dake faruwa tsakanin fulani makiyaya da manoma. 

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel