Binciken masana ya nuna Boko Haram ta kara karfi a 2017 fiye da a 2016

Binciken masana ya nuna Boko Haram ta kara karfi a 2017 fiye da a 2016

- Mutane sama da dubu suka kashe a 2017

- Kasa da haka suka kashe a 2016

- Ana tsoron zasu kara karfi a bana 2018

Binciken masana ya nuna Boko Haram ta kara karfi a 2017 fiye da a 2016
Binciken masana ya nuna Boko Haram ta kara karfi a 2017 fiye da a 2016

Bincike da BBC ta gudanar, na kididdigar rahotannin hare haren ta'addanci a 2016 da 2017, ya nuna cewa, kungiyar kara karffi tayi maimakon durkushewa, duk da kudi da ake ware wa domin tsaro a shekarun nan.

An kasa kama Shekau Abubakar shugaban Boko Haram, da ma mataimakansa, da kuma wadanda suka balle suka kafa tasu kungiyar, watau Al-Barnawi.

Saboda tsoron Buhari a farkon mulkinsa, kungiyar ta nemi dauki daga kungiyar 'yan ta'adda ta ISIL, inda su kuma suka yi wa shugaban juyin mulki suka nada wani, shi kuwa, yayi musu tawaye ya koma Haramun dinsa.

DUBA WANNAN: Za'a yi wa mutum miliyan 25 riga-kafin allurar masassara

An dai sami asarar akalla mutane 20,000 a haren-haren na kungiyar, kuma da yawa sun tsere daga yankin.

Ga alama dai kungiyar zata ci wannan zamani tana addabar yankinkamar yadda na Taliban suka kwashe shekaru kusan 50 suna addabar kasar Afghanistan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel