Nigerian news All categories All tags
Shugaban kasa Buhari ya shiga taro na musamman da Gwamnonin Jihohi

Shugaban kasa Buhari ya shiga taro na musamman da Gwamnonin Jihohi

- Shugaban kasa Buhari ya sa labule da wasu Gwamnoni

- Gwamnoni 6 ne ke ganawa da Buhari yanzu a cikin Villa

- Hakan na zuwa ne bayan wasikar da Obasanjo ya rubuta

Yanzu mu ke jin cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sa labule da Gwamnonin Jihohin kasar nan a fadar sa. Hakan na zuwa ne jim kadan bayan wasikar tsohon Shugaban kasa Oluesgun Obasanjo. Dazu Shugaban ya gana da Hafsun Sojoji.

Shugaban kasa Buhari ya shiga taro na musamman da Gwamnonin Najeriya

Shugaba Buhari tare da wasu Gwamnoni kwanaki

Shugaba Buhari yana ganawa da wasu daga cikin Gwamnonin kasar ne a Aso Villa. An fara zaman ne tun wajen karfe 2:00 na rana. Wani Hadimin Shugaban kasar Bashir Ahmaad ya tabbatar da wannan a shafin sa na Tuwita.

KU KARANTA: Babban 'Dan Majalisar Dattawa ya leka Jihar Benuwe

Rahotannin da ke zuwa mana sun tabbatar da cewa Shugaba Buhari ya shiga zantawa ne da Gwamnoni 6 na kasar wanda su ka hada da Shugaban Gwamnonin kasar watau Mai Girma Abdulaziz Yari na Jihar Zamfara.

Sauran Gwamnonin sun hada da Udom Emmanuel na Jihar Akwa Ibom, sai Gwamna Dave Umahi na Ebonyi da Rt. Hon. Aminu Masari na Katsina, da Simon Lalong na Filato da kuma Gwamnan Jihar Kebbi watau Sanata Atiku Bagudu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel